Isa ga babban shafi

‘Yan Sanda sun kama mutane 2 a Ireland dake kokarin karbar fansho

‘Yan Sanda a kasar Ireland sun kama wasu mutane biyu da ake tuhuma da daukar gawar wani mutum zuwa ofishin gidan waya domin karbar kudin fanshon sa.

Kudin Euros
Kudin Euros AFP/ Pedro ARMESTRE
Talla

Rahotanni sun ce jami’an gidan yarin sun ki amincewa da bukatar mutanen biyu na karbar kudin fanshon a madadin mamacin wanda suka ce bashi da lafiya, abinda ya sa suka dauki gawar sa, suka sanya a mota domin kai shi inda ake biyan kudin.

Daya daga cikin mutanen biyu yace lokacin da suka dauki mutumin mai shekaru 66 daga gidan sa yana da rai, saboda haka suna da yakinin a gidan wayar ya mutu lokacin da yake jiran karbar kudaden.

Takardar kudin Euro
Takardar kudin Euro pmfd / Getty images

‘Yan sanda sun yi watsi da matsayin wadannan mutane, inda nan take aka kama su, domin ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin.

Jami’an tsaro a kasashen yammacin duniya na zargin iyalai da dama da zamba cikin aminci wajen karbar kudaden fanshon mutanen da suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.