Isa ga babban shafi
Amurka-Afghanistan

Biden zai raba kadarorin Afghanistan ga wadanda harin 9/11 ya rutsa da su

Shugaban amurka US President Joe Biden ya kwace kadarorin da suka kai na dala biliyan 7, mallakin tsohuwar gwamnatin Afghanistan a juma’a, inda ya ce yana da niyyar rarrabawa ga wadanda hare haren 9 ga wataan Satumba suka rutsa da su, da kuma wadanda yaki ya rutsa da su a kasar Afghanistan da ke neman taimako.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. AP - Andrew Harnik
Talla

Wannan mataki ya janyo mummunan martini daga sabuwar gwamnatin Afghanistan, karkashin kungiyar Taliban, wadda ta bayyana wannan kwace a matsayin sata, da kuma alamun rashin tarbiyya daga Amurka.

Kudaden da wani jami’in Amurka ya ce an  samo su ne daga tallafi daga kasashen ketare ga gwamnatin Afghanistan da ke samun goyon bayan kasashen yamma a lokacin, suna jibge ne a baitulmalin Amurka tun a shekarar da ta gabata, a lokacin Taliban ta samu nasarar karbe mulkin kasar.

Fadar gwamnatin Amurka ta ce rabin kudaden da aka karbe din zai shiga asusun wata gidauniya ta jinkai don taimaka wa al’ummar Afghanistan da makomarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.