Isa ga babban shafi
Iran - Nukiliya

An dakatar da tattaunawar nukiliyar Iran bayan bukatar Rasha

Kungiyar EU ta ce dole a dakatar da tattaunawar da ta ke jagoranta kan farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015 da wasu kasashen duniya, saboda wasu sabbin bukatu da Rasha ta gabatar masu tsarkakiya ga tattaunawar.

Kungiyar EU ta ce dole a dakatar da tattaunawar da ta ke jagoranta kan farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015 da wasu kasashen duniya, saboda wasu sabbin bukatu da Rasha ta gabatar masu tsarkakiya ga tattaunawar.
Kungiyar EU ta ce dole a dakatar da tattaunawar da ta ke jagoranta kan farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015 da wasu kasashen duniya, saboda wasu sabbin bukatu da Rasha ta gabatar masu tsarkakiya ga tattaunawar. AP - Vahid Salemi
Talla

Shugaban manufofin Ketare na Kungiyar Tarayyar Turai EU Josep Borrell ya wallafa dakatar da tattaunawar ta shafinsa na twitter, saboda wasu dalilai masu alaka da bukatun Rasha" duk da cewa "daftarin karshe dangane da batun na kan teburi".

Tun a karshen watan Nuwamba ne aka fara tattaunawar tsakanin kasashen Birtaniya da China da Faransa da Jamus da Iran da kuma Rasha, sai kuma Amurka da ta shiga tattaunawar a kaikaice.

Kafin wannan sanarwa dai, sun kaiga fahimtar juna a akasarin manufofinsu kan farfaɗo da yarjejeniyar da kasashen suka cimma da Iran a shekarar 2015, wanda ya fara warwarewa lokacin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fice daga cikinta a cikin 2018.

Sai dai a makon da ya gabata Rasha ta ce tana neman a ba ta tabbacin cewa takunkumin da kasashen yamma suka kakaba wa tattalin arzikinta bayan mamayewar da ta yi wa Ukraine ba zai shafi kasuwancinta da Iran ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.