Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai-Ukraine-Rasha

Tarayyar Turai na tunanin jingine karbar Ukraine a NATO

Shugabanin kasashen Turai dake gudanar da wani taron su a birnin Versailles na Faransa sun bayyana cewa yanzu zancen saka Ukraine a cikin kasashen NATO bai taso ba, sanarwar dake zuwa a daidai lokacin da dakarun Rasha ke ci gaba da sa kai zuwa babban birnin kasar Kiev.

Tutocin kasashen tarayyar Turai gabanin taron shugabanninta a birnin Versailles na Faransa.
Tutocin kasashen tarayyar Turai gabanin taron shugabanninta a birnin Versailles na Faransa. REUTERS - SARAH MEYSSONNIER
Talla

Hukumomin Rasha na zargin Amurka da hukumomin Ukraine da gudanar da aiki tare don samar da makamin kare dangi a Ukraine, labarin da kasashen biyu suka musanta nan take.

Ko a  2018, hukumomin Rasha sun zargi Amurka da gudanar da wasu ayyuka a boye a wasu cibiyoyin sarrafa makamshin Nukiliya dake kasar Geogia,kasar ta Geogia dake ruwa da tsaki yanzu haka na ganin ta shiga jerryn kasashen Nato.

A daya gefen yanzu haka, kasashen kungiyar  tarrayar Turai  dake gudanar da taron shugabanin kasashen a Versailles dake Faransa ganin tsanantar yaki dake gudana a Ukraine, sun bayyana cewa ya zama wajibi su jingine batun saka kasar ta Ukraine a jerin kasashen kungiyar tsaro ta Nato.

Dakarun Rasha na daf da kama babban birnin kasar Ukraine inda rahotanni ke nuni da cewa suna kokarin yi wa babban birnin kasar kawanya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.