Rasha ta tilastawa 'yan Ukraine fiye da miliyan 4 gudun hijira - MDD
Sabbin alkaluman da majalisar dinkin duniya ta fitar sun nuna cewar ‘yan Ukraine kusan miliyan 4 da dubu 100 ne suka tsere daga kasarsu, tun bayan yakin da Rasha ta kaddamar a ranar 24 ga watan Fabarairu, inda a yanzu haka dubun dubatar ‘yan kasar ta Ukraine ke kwarara zuwa kasashe makwaftansu.
Wallafawa ranar:
Yayin karin bayani kan hain da ake ciki, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce ‘yan Ukraine miliyan 4 da dubu 137 da 842 ne suka tsere daga kasar cikin makwanni biyar da ‘yan kwanaki, alkaluman da ke nuna samun karin ‘yan gudun hijira dubu 34 da 966.
Hukumar ta UNHCR da kara da cewar kashi 90 cikin 100 na yawan ‘yan gudun hijirara na kasar Ukraine Mata ne da kananan yara.
Ita kuwa hukumar kula da kaurar baki ta majalisar Dinkin duniya IOM, ta fitar da rahoton da ke cewa wadanda ba ‘yan kasar Ukraine ba kusan dubu 205 ne suka tsere daga kasar, tun bayan yakin da Rasha ta kaddamar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu