Isa ga babban shafi

Abramovich na cikin tsaka mai wuya bayan kwace kadarorinsa a Birtaniya

Bayanai daga wasu majiyoyi kwarara wadanda kawo yanzu ba a tabbatar ba a hukumance s un ce hamshakin attajirin nan dan kasar Rasha Roman Abramovich ya shiga mawuyacin hali tun bayan da gwamnatin Birtaniya ta kwace kadarorinsa a makwannin baya, sakamakon mamaye Ukraine da kasarsa Rashan ta yi.

Roman Abramovich hamshakin attajiri dan kasar Rasha da ya mallaki kungiyar Chelsea.
Roman Abramovich hamshakin attajiri dan kasar Rasha da ya mallaki kungiyar Chelsea. AP - Martin Meissner
Talla

Yanzu haka dai rahotanni sun ce, Abramovich na shirin fara tuntubar abokansa attajirai domin samun aron kudi cikin gaggawa.

A halin da ake ciki dai, Abramovich na kokarin sayar da kungiyarsa ta Chelsea, duk da dai babu tabbas kan tsarin da za a bi wajen aiwatar da wannan ciniki, ba tare da gwamnati ta karbe iko da kulob din da ke birnin Landan ba.

A cewar wani rahoto da jaridar Sun ta buga, Abramovich na neman aron zunzurutun kudi kusan fam miliyan daya domin cigaba da biyan wasu hadimansa albashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.