Isa ga babban shafi

Rasha ta ce ta kama 'yan Birtaniya masu taya Ukraine yaki

Kafar talabijin din Rasha ta watsa faifan bidiyo na wasu ‘yan Britaniya da aka kama suna taya Ukraine yaki, inda suke bukatar Firayim Minista Boris Johnson ya shiga tattaunawa da Rasha don a sako su.

Wasu sojojin Rasha masu yaki a Ukraine
Wasu sojojin Rasha masu yaki a Ukraine REUTERS - THOMAS PETER
Talla

Mutanen biyun da aka bayyana sunayensu Shaun Pinner da Aiden Aslin, sun nemi a yi musanyar su da Viktor Medvedchuk, wani attajiri dan kasar Ukraine kuma makusancin Shugaba Vladimir Putin, wanda aka kama a kwanan baya a kasar. 

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Biritaniya ta fitar, 'yan uwan ​​Pinner sun tabbatar da cewa sojojin Rasha suna tsare da mutanen biyu.

Sanarwar ta kara da cewa iyalan mutanen biyu suna aiki tare da ma'aikatar don tabbatar da 'yancinsu yayin da ake amfani da yarjejeniyar Geneva da ta shafi fursunonin yaki.

Dama dai ita kanta Ukraine ta watsa wani video na attajirin, akan a yi musanyar sa ta hanyar kwashe fararen hula da sojoji daga birnin Mariupol da Rasha ta yi wa kawanya.

A baya dai fadar Kremlin ta yi watsi da ra'ayin musanya shi da 'yan kasar Ukraine da Rasha ke tsare da su, yayinda Zelensky ya dage akan hakan.

Ukraine dai na zargin makusancin na Putin da cin amanar kasa da yunkurin satar albarkatun kasa daga Crimea da Rasha ta mamaye da kuma mika sirrin sojojin Ukraine ga Moscow.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.