Halin da mutane ke ciki a gabashin Ukraine na da matukar tayar da hankali - MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta ce halin da ake ciki a gabashin Ukraine, musamman dangane da ayyukan jin kai, yana da matukar tayar da hankali, tare da gargadin cewa lamurra na kara kazancewa watanni hudu bayan mamaye kasar da Rasha ta yi.
Wallafawa ranar:
Sanarwar hukumar kula da ayyukan jinkai ta majalisar dinkin duniya OCHA ta ce al’amura sun fi kazancewa a Donbas da kuma Severodonetsk dake gabashin Ukraine.
Daruruwan fararen hula ake kyautata zaton sun makale a birnin na Severodonetsk, inda ake sa ran wasunsu sun samu fakewa a masana'antar sinadarai ta yankin.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana samun raguwar samun ruwa mai tsafta, abinci, tsaftar muhalli da wutar lantarki a birnin, matsalolin da suka yi mummunar illa ga fararen hula, ciki har da ma'aikatan agaji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu