Isa ga babban shafi

Za a ci gaba da fama da tsananin zafi a Turai har zauwa 2060

Tsananin zafi da ke damun kasashen Turai na kara yawaita kuma akwai yuwuwar ci gaba da samun sa har zuwa nan da shekaru 2060, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Yanayin tsananin zafi a turai ya kai matakin da ba a taba gani ba.
Yanayin tsananin zafi a turai ya kai matakin da ba a taba gani ba. REUTERS - STEPHANE MAHE
Talla

Yanayin zafin a yanzu na tayar da hankali ga kasashen da ke fitar da turirin masana’antu mai gurbata muhalli, in ji shugaban hukumar kula da yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya Petterri Taalas.

Tsananin zafin ne dai ya kara rura wutar daji wanda ya sanya samun samada digiri 40 a ma'aunin celcius a karon farko a Biritaniya.

Robert Stefanski, babban jami'in kula da sauyin yanayi na hukumar kula da yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce, ana sa ran fuskantar tsananin zafi a Faransa da Burtaniya da kuma yuwuwar hakan a Switzerland, inda kuma a ke ganin yiwuwar ci gaba da fuskantar hakan har zuwa tsakiyar mako mai zuwa.

A shekarar da ta gabata ne aka karya tarihin zafi a Turai, lokacin da ma'auni ya kusa 49 a yankin Sicily da ke kudancin Italiya.

Maria Neira, shugabar sashin kula da muhalli da sauyin yanayi da kuma kiwon lafiya, ta yi la’akari da yadda tsananin zafi a Turai a shekarar 2003 ta janyo asarar rayuka sama da 70,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.