Isa ga babban shafi

Hukumomin Girka sun kwashe mutane daga yankin Lesbos

A yankin Lesbos na kasar Girka, jam’ian kwana-kwana sun yi amfani da jirage 7 da wani jirgi mai saukar ungulu  wajen kai dauki  tare da kwashe  jama’a na yankin da baki yan yawon bude ido da wutar daji ta ritsa da su a wannan tsibiri da ya sha’ara  wajen karbar baki yan yawon bude ido.

Tsibirin Lesbos
Tsibirin Lesbos REUTERS - ELIAS MARCOU
Talla

Hukumomin yankin sun bayyana cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe 10 agogon kasar  a yau asabar,rashin kyawon yanayi da iska su taimakawa wuta bazuwa zuwa wasu yankuna cikin dan kankanin lokaci.

Tsibirin Lesbos
Tsibirin Lesbos AFP

Al’amarin da ya sa magajin garin yammacin Lesbos Taxiarchis Verros bada umurni kwashe mutanen yankin cikin gaggawa, ba tareda bada adadin mutanen da aka samu nasarar kwashewa daga wannan yankin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.