Isa ga babban shafi

Kotun Finland ta umarci Gibril Massaquoi na Liberia ya sake gurfana gabanta

Wata kotu a kasar Finland ta umarci Gibril Massaquoi wanda ake zargi da haddasa yakin basasa a kasar Laberia ya gurfana gabanta, watanni bayan wanke shi da wata kotu ta yi.

Massaquoi ya taba zama babban kwamandan kungiyar 'yan tawayen Saliyo RUF da ta yi yaki a Laberia.
Massaquoi ya taba zama babban kwamandan kungiyar 'yan tawayen Saliyo RUF da ta yi yaki a Laberia. © Francois Mori / AP
Talla

Za a fara shari'ar ce a birnin Turku na kasar Finland a ranar 10 ga watan Janairu, daga bisani kotun ta ziyarci kasashen Laberia da Saliyo don sauraron shaidu, kafin kuma a koma kasar Finland.

Massaquoi, wanda ya koma kasar Finland a shekara ta 2008, ana zarginsa da laifukan da suka hada da fyade da kisan gilla da kuma daukar yara aikin soja.

A watan Afrilun da ya gabata ne wata kotu a Finland ta wanke Massaquoi, ta na mai cewa masu gabatar da kara ba su tabbatar da hannun sa a laifukan da ake zarginsa da aikatawa a shekarun baya na yakin Laberia na biyu da aka kawo karshen sa a shekara ta 2003 ba.

Sai dai masu gabatar da kara a Finland sun daukaka kara kan hukuncin zuwa kotun daukaka kara da ke kasar.

Massaquoi ya taba zama babban kwamandan kungiyar 'yan tawayen Saliyo RUF da ta yi yaki a Laberia.

Ya musanta dukkan tuhume-tuhumen inda ya ce wanda ake tuhumar baya  Laberia lokacin da aka aikata laifukan da ake zargin sa, sai dai kuma an kama shi a Finland a shekarar 2020 bayan wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta gudanar da binciken tarihin yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.