Isa ga babban shafi

Faransa za ta haramtawa dalibai sanya hijabi da abaya a Makarantu

Ma’aikatar ilimi a Faransa ta sanar da shirin fara haramtawa dalibai sanya hijabi a makarantun kasar, matakin da ake ganin zai haddasa dambarwa lura da karuwar mabiya addinin Islama a sassan kasar.

Wata daliba sanye da Hijabi.
Wata daliba sanye da Hijabi. © Sabiha Cimen
Talla

Dai dai lokacin da ake shirin komawa makarantu a sassan Faransa kafofin yada labarai sun ruwaito ministan ilimi na kasar Gabriel Attal na cewa za a harantawa dalibai mata amfani da rigunan Abaya da galibi mabiya addinin Islama kan yi amfani da su wajen rufe jikinsu.

A cewar ministan makarantun Faransa karkashin dokokin da aka samar tun a karni na 19 basu sahale amfani da duk wani nau’in nuna addini ko al’adu a makarantun kasar ba.

Ma’aikatar Ilimin ta bayyana cewa haramcin zai shafi amfani da Hijabi ko dan kwalin da ake rufe kai ko kuma manyan rigunan abaya da kan rufe jikin mata.

Bayan matakin mahukuntan Faransa na haramtawa dalibai a dukkan matakai amfani da duk wani nau’in dan kwali ko mayafi da ke rufe kai a shekarar 2004, a 2010 kasar ta kafa dokar haramta amfani da nikabi ko kuma mayanin da ke kulle fuska, sai dai a wannan karon ana ganin batun zai haddasa tarnaki.

Zuwa yanzu akwai Musulmin da yawansu ya kai miliyan 5 a sassan Faransa da kaso mai yawa ‘yan asalin kasar.

A wata zantawarsa da gidan talabijin na TF1 ministan ilimin na Faransa Gabriel Attal ya kafa hujja da cewa bai kamata idan malami ya shiga aji bayar da darasi ya rika gane addinin dalibai kawai da kallonsu ba.  

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan shafe tsawon watanni ana tafka muhawara game da yunkurin na haramta dalibai musulmi amfani da rigunan na Abaya da mayaki bayan tun farko an haramta amfani da Hijabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.