Ministan shari'ar Faransa zai amsa kiran kotu, bisa zarginsa da cin zarafi
Bayanar Minista mai ci a kotu, lamari ne da ba a taba ganin irinsa ba a Faransa. Daga ranar litinin, Ministan shari'a na yanzu, Eric Dupond-Moretti, zai kasance tsawon kwanaki goma a gaban wata kotu, ana zarginsa da cin zarafi a matsayinsa na minista a zantukan da suka jibanci ayukan kotu da ke da alaka da aikin sa na lauya a baya.
Wallafawa ranar:
Zaman shara’a da za a soma a gaban kotun shari'a ta jamhuriya (CJR), wadda ita kadai ce aka ba izinin gurfanar da mambobin gwamnati bisa laifukan da suka aikata wajen gudanar da ayyukansu, ranar Litinin ake kyautata zaton Ministan shara’ar Faransa zai kasance gaban alkalan` kotun birnin Paris.
Ministan zai ci gaba da gudanar da aikinsa duk da tuhumar da ake masa, har zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba.
Firaminista kasar ta Faransa Elisabeth Borne ta sanar da cewa "dole ne Eric Dupond-Moretti ya sami lokacin da ya dace don kare kansa."
Idan aka same shi da laifin "ba da son rai", zai fuskanci zaman gidan yari na shekaru biyar da tarar Yuro 500,000, da kuma karin hukuncin rashin cancanta da kuma haramta masa rike mukaman gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu