Mutane uku suka mutu a hatsarin jirgin sama mai taimakawa wajen kashe gobara
Mutane uku ne suka mutu bayan da wani karamin jirgin sama ya yi hadari a arewacin kasar Australia a yau Asabar yayin da yake taimakawa wajen kashe gobarar daji a fakaice, in ji ma'aikatan agajin gaggawa.
Wallafawa ranar:
Minti 1
Talla
Jirgin ya fado ne a kusa da garin McKinlay da ke da nisan fiye da kilomita 1,600 a arewa maso yammacin Brisbane.
Hukumar ta ce jirgin da fasinjansa na aikin taswirar gobarar. Fiye da gobara goma aka samu a jihar Queensland.
Hukumar kula da sufuri ta Australia za ta binciki musabbabin hadarin.
Australia na fuskantar lokacin da ake fama da tashin gobarar daji tun daga shekarar 2019-2020, ya yi aman wuta da gandun daji a gabar tekun gabas, inda ya kashe miliyoyin dabbobi tare da lullube garuruwa da hayaki mai cutarwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu