Isa ga babban shafi

Matsalar mutuwar mata yayin haihuwa ta kai kololuwa a Birtaniya

Wani rahoto da kwararru suka fitar a yau Alhamis ya bayyana karuwar alkaluman matan da ke mutuwa a Birtaniya lokacin haihuwa, alkaluman da masana ke cewa shi ne mafi kaiwa kololuwa da kasar ta gani cikin fiye da shekaru 20 da suka gabata.

Alkaluman sun nuna cewa fiye da kashi 3 cikin mata dubu 100 da ke haihuwa a Birtaniya na rasa rayukansu daga bara zuwa bana.
Alkaluman sun nuna cewa fiye da kashi 3 cikin mata dubu 100 da ke haihuwa a Birtaniya na rasa rayukansu daga bara zuwa bana. © Ural Press / AP
Talla

Alkaluman wanda MBRRACE-UK ta fitar a yau, kungiyar da ke sanya idanu kan mutuwar mata da kananan yara a Birtaniya ta ce yanayin mutuwar mata a lokacin haihuwa da kuma jarirai sabbin haihuwa ta kai kololuwar da kasar ba ta taba gani ba tun bayan daukar tsauraran matakan bayar da cikakkiyar kariya da mabanbantan rigakafi ga mata masu juna kusan shekaru 20 da suka gabata.

Kungiyar ta ce duk da kasancewar Birtaniya kasa mafi karancin ganin mutuwar kananan yara a duniya, amma a baya-bayan nan alkaluman matan da ke mutuwa musamman daga bara waccan zuwa bana, na ci gaba da kaiwa kololuwar da kasar bata taba gani ba, duk da cewa yawaitar mace-macen ya fi tsananta tsakanin wasu tsiraru.

Wannan karuwar alkaluma na zuwa bayan zarge-zargen da ya dabaibaye asibitocin Shrewsbury da Telford Hospital Trust na yammacin Ingila wadanda ake zarga da sabbaba mutuwar jarirai sabbin haihuwa 201 da kuma mata masu ciki 9  cikin shekaru 20.

Wannan sabbin alkaluma a cewar ma’aikatar lafiyar Birtaniya ya tilasta karfafa kiraye-kirayen ganin an kara zuba kudi don kare lafiyar mata da jariran tare da baiwa jami’ai horo na musamman a bangaren.

MBRRACE-UK ta bayyana cewa daga 2020 zuwa 2022 jarirai ko iyaye 13.41 cikin dubu 100 ke mutuwa ko dai a wajen haihuwa ko kuma yayin rainon ciki.

Hukumar lafiyar Birtaniya, ta ce bayan kisan Covid-19 ta yiwa masu juna biyu a kasar wannan ne karon farko da ake ganin yawaita mata masu mutuwa a lokacin goyon ciki ko haihuwa.

A cewar kungiyar alkaluman mata da jariran da ke mutuwa na karuwa shekara-bayan shekara wanda ya sanya bukatar daukar matakai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.