Isa ga babban shafi

Akalla mutane 10 suka mutu sakamakon harin da Rasha ta kai yankin Odessa

A yau Lahadi aka gano wata mata da wani jariri dan watanni takwas a cikin baraguzan ginin da wani jirgin saman Rasha mara matuki ya kai hari ta sama  a birnin Odessa, wanda ya kai adadin mutanen da suka mutu ya kai goma, kamar yadda hukumomin Ukraine suka tabbatar.

Yankin Odessa a kasar Ukraine
Yankin Odessa a kasar Ukraine © Дмитро Долматов / RFI
Talla

Wannan harin da aka kai kan wani gini mai hawa tara da ke wannan tashar jiragen ruwa a tekun Black Sea ya girgiza mazauna garin a cewar gwamnan Odessa,Oleg Kiper.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Ukraine ta tabbatar da mutuwar mutane goma.

Yankin Odessa na kasar Ukraine
Yankin Odessa na kasar Ukraine © Oleksandr Gimanov / AFP

Sun kuma tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da aikin bincike da kuma "share" wuraren da wannan ginin ya ruguje.

Sai dai hukumomin kasar ba su bayar da rahoton adadin wadanda suka jikkata ba, ko da yake hukumar bayar da agajin gaggawa ta bayyana wasu mutane takwas da suka jikkata a yammacin jiya Asabar.

Jama’ar garin na Odessa na jimamin wadanda harin na Rasha ya rutsa da su.

Wasu daga cikin baraguzan ginin da ya rushe a yankin Odessa
Wasu daga cikin baraguzan ginin da ya rushe a yankin Odessa AP

A ranar Asabar, shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya soki a cikin jawabinsa Rasha da kuma dangantata da kasar ‘yan "ta'adda.

Shugaban kasar Ukraine ya sake yin kira ga kawancen kasashen yammacin Turai da su taimaka da kuma kawo nasu agaji da sauri, da makaman kare dangi - wadanda Kiev ke da karancinsa da jiragen yaki don dakile sojojin Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.