Isa ga babban shafi

Daga wannan Litinin mazauna Jamus za su samu damar busa tabar wiwi

Jamus za ta halatta wani bangare na amfani da tabar wiwi a cikin kasar daga ranar litinin mai zuwa, a wani mataki ne aiwatar da alƙawarin gwamnatin haɗin gwiwar shugaba Olaf Scholz.Sai dai halascin ba zai zama sakin mara a yi amfani da ganyen kai tsaye cikin sauki ba ko kara zube ba.

Wani mutum ya kunna taba wiwi yayin da masu fafutuka tabar wiwi suka taru don bikin ranar cannabis na shekara-shekara na duniya da kuma zanga-zangar neman halatta tabar wiwi, a gaban Ƙofar Brandenburg, a Berlin, Jamus, Afrilu 20, 2022. REUTERS/Lisi Niesner
Wani mutum ya kunna taba wiwi yayin da masu fafutuka tabar wiwi suka taru don bikin ranar cannabis na shekara-shekara na duniya da kuma zanga-zangar neman halatta tabar wiwi, a gaban Ƙofar Brandenburg, a Berlin, Jamus, Afrilu 20, 2022. REUTERS/Lisi Niesner REUTERS - LISI NIESNER
Talla

Ga wasu daga cikin ka’idojin:

Daga ranar 1 ga watan Afrilu, doka za ta bai wa mazauna Jamus damar ɗaukar busasshen tabar wiwi har gram 25 don amfanin ƙashin kai, wanda zai isa kusan kara 80.

Haka kuma sabuwar dokar za ta ba da izinin noman tabar wiwi a cikin gida, amma dashe tsirrai uku kacal ga kowane balagegge ko gram 50 na busasshiyar tabar wiwi.

Haramci

Busar tabar za ta ci gaba da zama haramun a mita 100 na harabar makarantu, filayen wasanni da taron jama’a.

Haka zalika, za'a hana shan tabar a hanyoyin tattakin jama’a tsakanin karfe 7:00 na safe zuwa 8:00 na yamma.

- A ina za’a sayer ta wiwi?

Daga ranar 1 ga watan Yuli, Jamus za ta kafa ƙungiyoyin noman wiwi don baiwa mutane damar samunsu baisa tsarin doka.

Kungiyoyin da za’a kira su da ‘Cannabis clubs’ za su ƙunshi mambobi 500 kowannensu kuma za su iya siyar da busasshiyar tabar wiwi gram 50 a kowane wata ga kowane memba.

Masu ƙasa da shekaru 21 za a iyakance su da gram 30 na tabar kowace wata saboda takaita su da kashi 10 na sinadaren THC da ke juya ƙwaƙwalwa.

Ƴan yawon bude ido -

Hanyoyi biyu kachal dokar ta bada damar samun taba wiwi, wato ka noma ta a gidanka ko kuma a fansa a samu a hannun ƙungiya, ga mazuna Jamus na akalla watanni shida.

Domin kawar da fargabar da jam'iyyun adawa ke da shi musamman kawancen CDU-CSU masu ra'ayin mazan jiya, da ke cewa sabuwar dokar za ta iya sahalewa ƴan yawon shakatawa masu ta’ammali da muggan kwayoyi cin karensu babu babbaka.

Gonar taba wiwi
Gonar taba wiwi © Cortesia do Tèla Non

Hakan sausauci ne ga bukatun da farko da gwamnatin Scholz ta Social Democrats da Greens da kuma FDP masu ra'ayin kasuwanci suka gabatar na barin a rika sayar da tabar wiwi a shaguna da manyan kantuna, matakin da EU ta yi fatali da shi.

Ko da yake yanzu haka doka ta biyu ta bada damar yin gwajin siyar da taba wiwi a a shaguna ko kantin magani a wasu yankuna.

- Sukar lamirin -

Gwamnati ta dage cewa sabuwar dokar za ta rage illar da ke tattare da taba wiwi saboda za ta magance matsalar gurbatattun abubuwa da aka samu cikin tabar a kasuwar bayan fage.

Sai dai kungiyoyin likitoci da kiwon lafiya sun soki dokar sosai.

Tuni Friedrich Merz, shugaban jam'iyyar masu ra'ayin rikau na 'yan adawa, ya yi gargadin cewa idan jam'iyyarsa  ta sake komawa mulki a 2025, to ko shakka babu za ta soke dokar nan take.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.