Haye da Chisora zasu fuskanci hukuncin Dauri a Jamus
Manyan ‘Yan Damben kasar Birtaniya Davd Haye da Dereck Chisora ga alamu zasu fuskanci hukunci dauri a kasar Jamus saboda damben bayan fage da suka yi a karshen mako. A ranar Assabar ne Haye da Chisora suka gwabza da juna bayan Chisora ya sha kashi hannun Vitali Klitschko zakaran Damben ajin masu nauyi na duniya.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka ana Tuhumar Haye ne da Yunkurin raunata Chisora, kuma zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari
Chisora ma ana tuhumar shi da yunkurin raunata Haye, kuma zai iya fuskantar hukuncin Daurin shekaru 5.
Sai dai Chisora wanda dan asalin kasar Zimbabwe ne ya aiko da sakon neman Gafara ga abun da ya faru tare da amsa yin ba daidai ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu