Isa ga babban shafi
Tennis

Nadal ya fice Wimbledon bayan ya sha kashi hannun Rosol

Rafael Nadal Zakaran Roland Garros ya fice gasar Wimbledon da ake gudanarwa a Birtaniya, bayan ya sha kashi hannun Lukas Rosol, na Jamhuriyyar Czech. Al’amarin da ya ba masoya kwallon Tennis mamaki game da ficewal dan wasan tun a zagayen Farko wanda ya lashe Roland Garros sau Bakwai.

Lukas Rosol na Jamhuriyyar Czech Republic a hannun hagu wanda ya doke  Rafael Nadal na Spain  a Wimbledon
Lukas Rosol na Jamhuriyyar Czech Republic a hannun hagu wanda ya doke Rafael Nadal na Spain a Wimbledon REUTERS/Toby Melville
Talla

Rosol wanda shi ne na 100 a ajin matsayin Tennis A duniya ya doke Nadal ne wanda shi ne na biyu a duniya.

An kwashe shekaru Biyar Rosol yana kai ziyara Wimbledon amma tun a zagayen Farko ne ake yin waje da shi. Amma a bana ga shi ya samu sa’ar yin mugun kashi.

A jiya alhamis dai an samu sabani a filinn Tennis inda Ivo Karlovic yace alkalan wasan sun ha’ince shi a wasan shi da Andy Murray na Birtaniya wanda ya lallasa shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.