Isa ga babban shafi
Tennis

Serena Williams ta karbi mukamin jarumar Tennis ta Duniya

Serena Williams ce ta daya a duniya duk da ta sha kashi a hannun Victoria Azarenka a Qatar Open, kafin ta kwace wa Azerenka matsayinta. Wannan ya ba Serena zama mace ta farko mai yawan shekaru da ke jagorancin ajin Matsayin Tennis a duniya.

Venus Williams 'Yar kasar Amurka rike da kofin da ta lashe a gasar US Open bayan doke Azarenka ta Belarus
Venus Williams 'Yar kasar Amurka rike da kofin da ta lashe a gasar US Open bayan doke Azarenka ta Belarus REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Serena ta samu rinjayen maki 265 fiye da Azerenka ta Belerus da kuma Maria Sharapova ta Rasha.

Bayan lashe Wimbledon da US Open a bara, Serena ta samu jimillar manyan kofunan gasar Tennis guda 15, wanda ya rage saura uku ta kamo kafar Martina Navratilova da Evert, wadanda ke bin Steffi Graf da ta lashe kofuna 22.

Ajin Matsayin Tennis

1. Serena Williams (Amurka) 10590 maki (+1)
2. Victoria Azarenka (Balarus) 10325 (-1)
3. Maria Sharapova (Rasha) 9715
4. Agnieszka Radwanska (Poland) 7750
5. Na Li (China) 6130
6. Angelique Kerber (Jamus) 5400
7. Sara Errani (Italiya) 4820
8. Petra Kvitova (Czech) 4510
9. Samantha Stosur (Australia) 3835
10. Caroline Wozniacki (Denmark) 3570

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.