Isa ga babban shafi
Bundesliga

Bayern Munich ta doke Stuttgart ci 2-1

Kungiyar Bayern Munich ta doke Stuttgart 2-1 wanda ya ba kungiyar damar buga wasanni 43 ba tare da samun galabarta ba karkashin sabon kocinta Pep Guardiola. Bayan kwashe lokaci suna kunne doki ci 1-1, Tsohon Dan wasan Barcelona Thiago Alcantara shi ne ya zirawa Bayern Munich kwallon da ya ba ta nasara, kuma kwallon shi ta farko a raga tun zuwan shi a kungiyar .

Thomas Mueller na Bayern Munich yana murza kwallo  a gasar Bundesliga
Thomas Mueller na Bayern Munich yana murza kwallo a gasar Bundesliga REUTERS/Ina Fassbender
Talla

Yanzu tazarar maki 13 ne Bayern Munich ta ba Bayer Leverkusen da ke matsayi na biyu, kuma tazarar maki 17 tsakaninta da Borussia Dortmund da ke matsayi na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.