An yi waje da Li Na a Roland Garros
‘Yar wasan Tennis ta kasar Faransa Kristina Mledenovic ta yi waje da Li Na ta China a gasar Rolland Garros da ake gudanarwa a Faransa bayan ta doke ta ci 7 da 5, 3 da 6, 6 da 1 a zagayen farko. Li Na ta taba lashe kofin gasar a 2011 kuma ita ce yanzu ke rike da kofin Australian Open.
Wallafawa ranar:
Dubban magoya bayanta ne suka aiko wa ‘Yar wasan da sakon jaje yawancinsu daga kasar China.
Haka ma ‘Yar kasar Belgium Yanina ta yi waje da Caroline Wozniacki, tsohuwar jarumar Tennis ta duniya.
Andy Murray da David Ferrer dukkaninsu sun tsallake zuwa zagaye na biyu bayan Murray ya doke Adrev na Kazakhstanm yayin da kuma Ferrer ya yi waje da Igor Sjsling na Holland.
A yau Laraba aka shiga kwanaki na hudu a gasar Rolland Garros babbar gasar Tennis. Kuma Roger Federer da Novak Djokovic da Maria Sharapova da Serena Williams zasu nemi tsallake wa zuwa zagaye na uku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu