Isa ga babban shafi
Tennis

Serena da Venus sun sha kashi a Roland Garros

Jarumar Tennis ta duniya Serena Williams ta sha kashi a hannun Garbine Muguruza ci 6 da 2, 6 da 2 a gasar Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa. Kuma wannan na zuwa ne bayan an yi waje da ‘yar uwarta Venus Williams a gasar.

Jarumar Tennis Serena Williams ta sha kashi a hannun Garbine Muguruza  a Roland Garros
Jarumar Tennis Serena Williams ta sha kashi a hannun Garbine Muguruza a Roland Garros REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Serena ita ce ta lashe kofin a bara amma Wannan ne karo na biyu da ake yin waje da Jarumar ta Tennis tun a tashin farko bayan ta taba shan kashi 2005 inda Anastasia ta Rasha ta doke ta a zagayen farko.

Yanzu dai Serena ta bi sahun Li Na ta China, jaruman tennis din da suka taba lashe kofin Roland Garros.

Sharapova ta Rasha ta tsallaka zagaye na uku bayan ta doke Tsvetana Pironkova ci 7 da 5, 6 da 2.

Haka ma Radwanska ta Poland ta tsallaka zuwa zagaye na uku bayan ta doke Karolina Pliskova ta Jamhuriyyar Czech.

Bangaren Maza.

Novak Djokovic ya doke Jeremy ci 6 da 1, 6 da 4, 6 da 2, haka ma Roger Federer ya tsallake zuwa zagaye na uku bayan ya doke Sebastian na Argentina.

A yau alhamis aka shiga kwanaki na biyar a gasar, kuma a yau Rafeal Nadal zai kara ne da Dominic na Australia, takwaransa kuma na Spain David Ferrer zai fafata da Simone Boleli na Italia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.