Isa ga babban shafi
CAN 2015

Algeria da Senegal sun doke Afrika ta kudu da Ghana

Kasashen Algeria da Senegal sun samu nasara a wasan farko da suka fafata a rukuninsu na C da ake ganin ya fi kowane rukuni zafi, bayan sun doke Afrika ta kudu da Ghana. Algeria ta doke Afrika ta kudu ne ci 3 da 1, yayin da kuma Senegal ta doke Ghana ci 2 da 1 a gasar cin kofin Afrika da ake gudanarwa a kasar Equatorial Guinea.

Senegal na fafatawa da Ghana a gasar cin kofin Afrika CAN 2015
Senegal na fafatawa da Ghana a gasar cin kofin Afrika CAN 2015 AFP PHOTO / CARL DE SOUZA
Talla

Yanzu Algeria ce ke jagorancin teburin rukuninsu da yawan kwallaye akan Senegal.
Ghana da Afrika ta Kudu dole sai sun yi kokarin samun nasara a wasansu na gaba a ranar Juma’a idan ba haka ba tun da wuri za a kore su a gasar.

A yau Talata kasar Cote d’Ivoire za ta fara fafatawa da Guinea, daga bisani kuma kasar Mali ta kece raini da Kamaru a rukuninsu na D

Tawagar Guinea a gasar sun bayyana gamsuwa da yadda aka tarbesu a kasar Equatorial Guinea duk da barazanar Ebola a kasarsu.

Kocin ‘yan wasan na Guinea Michel yace babu wani banbanci da aka nuna masu saboda Ebola, bayan an gudanar da gwaje gwaje a lokacin da suka iso Malabo.

Kasar Guinea dai tana cikin kasashen da ke fama da cutar Ebola, kuma saboda barazanar cutar ne Morocco ta ki karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon Afriika a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.