Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya ci kwallonsa ta 89 a gasar zakarun Turai

A karawar da Real Madrid ta doke Roma da ci 2-0 a jiya Laraba, dan wasan Real Madrid, Christiano Ronaldo ya zura kwallonsa ta 89 a gasar cin kofin zakarun Turai, kuma ta 12 a wanann kakar.

Cristiano Ronaldo na Real Madrid
Cristiano Ronaldo na Real Madrid REUTERS/Juan Medina
Talla

Ronaldo ne ya fara zura kwallo a ragar Roma kafin daga bisani Jese ya saka ta shi.

Wannan nasarar da Real Madrid ta samu wata gagarumar dama ce a gare ta, ta kaiwa matakin wasan dab da na kusan karshe, wato quarter final a gasar ta zakarunTurai.

Yanzu dai nanda makwanni uku Roma za ta kai ziyara Santiago Bernabeu domin karawa da Real Madrid a wasa na biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.