Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta sabunta kwangilar Neymar

Dan wasan Brazil Neymar zai ci gaba da bugawa Barcelona kwallo bayan ya kulla sabuwar yarjejeniya ta shekaru biyar da kungiyar da ke rike da kofin La liga. Kwangilar Dan wasan yanzu zata kawo karshe ne a 2021. 

Neymar na Brazil da ke taka leda a Barcelona ta Spain
Neymar na Brazil da ke taka leda a Barcelona ta Spain Foto: Reuters
Talla

Sanarwar da Barcelona ta fitar tace dan wasan zai karbi kudi euro Miliyan 200 a shekara ta farko, a shekara ta biyu zai karbi miliyan 222 na euro, sauran shekaru uku kuma zai karbi miliyan 250.

Tsohuwar kwangiilar Neymar za ta kawo karshe ne 2018, bayan Barcelona ta karbo dan wasan daga Santos ta Brazil a 2013.

Dama tun da farko shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeau ya yi watsi da rade-radin cewa Neymar zai koma Manchester United domin ci gaba da murza leda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.