Isa ga babban shafi
CAF

Kamaru ta doke Guinea Bissau

Kamaru ta doke Guinea Bissau ci 2 da 1 a karawar da suka yi jiya a gasar cin kofin Afrika da ake gudanarwa a kasar Gabon. Yanzu Kamaru ce saman teburin rukuninsu na A da maki hudu.

Kamaru ta dare teburin rukunin A da maki hudu
Kamaru ta dare teburin rukunin A da maki hudu RFI/Pierre René-Worms
Talla

Gabon ta rike Burkina Faso ci 1 da 1, a fafatawar da suka yi, kuma yanzu dukkaninsu suna da maki biyu ne a teburin rukuninsu na A.

A karawa ta gaba Kamaru za ta hadu ne da Gabon, wasan da zai yi zafi, domin Gabon da ke karbar bakuncin gasar za ta yi kokarin ganin Kamaru ba ta ci ta ba don kada ta fice gasar tun a zagayen farko.

Guinea Bissau da Burkina Faso za su yi kokarin samun nasara domin tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.