Isa ga babban shafi
Wasanni

Marcelo ya sabunta yarjejeniya da Real Madrid

Mataimakin Kaftin din Real Madrid Marcelo, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tsawaita zamansa a kungiyar har zuwa shekara ta 2022.

Mataimakin Kaftin din Real Madrid Marcelo, yayinda alkalin wasa Alejandro Jose Hernandez ya bashi jan kati yayin wasansu da Levente.
Mataimakin Kaftin din Real Madrid Marcelo, yayinda alkalin wasa Alejandro Jose Hernandez ya bashi jan kati yayin wasansu da Levente. REUTERS/Susana Vera
Talla

Marcelo mai shekaru 29, ya shafe shekaru 11 a Madrid, kuma ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofunan gasar zakarun nahiyar turai 3, da kuma kofunan gasar Laliga 4.

A jimlace Marcelo ya bugawa real Madrid wasanni 400 tun bayan shigarsa kungiyar a shekara ta 2006.

Sai dai a halin yanzu dan wasan ba zai bugawa Madrid wasannin la-liga har biyu a jere ba, saboda katin da aka bashi a wasan da suka tashi 1-1 tsakaninsu da Levente.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.