Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi ya ci kwallonsa ta 500

Gwarzon dan wasan kwallon kafar nan mai taka leda a Barcelona, Lionel Messi ya zura kwallonsa ta 500 a rayuwarsa ta wasan kwallon kafa.

Lionel Messi na Barcelona
Lionel Messi na Barcelona Reuters/Toby Melville
Talla

Messi dai ya ci wannan kwallon ne a fafatawar da Valencia ta doke Barcelona da ci 2-1 a gasar La Liga ta kasar Spain.

Duk da dai kwallon da Messi ya ci, hakan bai sa Barcelona ta kai ga gaci ba, kuma a karo na farko kenan tun shekara ta 2003 da kungiyar ta yi rashin nasara sau uku a jere  a gasar ta La Liga.

Watanni biyu da suka gabata, Barcelona ta caccasa Valenica da ci 7-0 a Camp Nou amma ana iya cewa yanzu kungiyar ta rama abinda aka yi ma ta.

Yanzu haka Atletico Madrid ta yi kan- kan-kan da Barcelona wajen maki, inda suke da maki 76. Sai dai duk da hakan Barcelona ce ke jan ragama a teburi.

Atletico dai ta samu karin maki ne bayan ta lallasa Granada da ci 3-0 kuma ta na da wasanni guda biyar da za ta yi nan gaba.

Ita kuwa Real Madrid na da maki 75, tazarar maki guda kenan tsakaninta da Barcelona da Atletico.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.