'Yan wasan Amurka sun yi alhinin harin Las Vegas
Kungiyoyin wasanni da dama a Amurka sun bayyana alhininsu game da kazamin harin bindiga da wani mutun mai shekaru 64 ya kai a birnin Las Vegas, in da ya kashe mutane akalla 58 tare da jikkata sama dsa 500 .
Wallafawa ranar:
'Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle da ‘yan wasan Tennis da kwallon kafa da suka hada da wadanda ke buga wasannin League a Amurka duk sun yi tir da wannan hari a shafukansu na sada zumunta.
Hukumar wasannin League ta kasar ta sanar da shirinta na karrama wadanda lamarin ya shafa gabanin fafatawa tsakanin kungiyoyi, domin ko a jiya sai da kungiyoyin Kansas City da Washington Redskins suka yi shiru na tsawon minti guda gabanin fafatawarsu a matsayin karramawa ga mamata a harin na bindiga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu