Isa ga babban shafi
Wasanni - Olympics

Tawagar kwallon kwandon Amurka ta kama hanyar lashe Zinare a Olympics

Tawagar kwallon Kwandon Amurka ta tsallaka matakin wasan karshe na gasar da ke gudana a wasannin motsa jiki na Olympics da japan ke karbar bakunci.

Tawagar kwallon kwandon Amurka yayin fafatawa da takwarorinsu na Jamhuriyar Czech a gasar Olympics da Japan ke karbar bakunci.
Tawagar kwallon kwandon Amurka yayin fafatawa da takwarorinsu na Jamhuriyar Czech a gasar Olympics da Japan ke karbar bakunci. REUTERS - BRIAN SNYDER
Talla

Amurka ta samu nasarar ce bayan doke Australia da kwallaye 97-78 yayin fafatawar da suka yi jiya Alhamis a zagayen wasan kusa da na karshe.

Kafin gasar bana dai, sau uku a jere Amurka ke lashe lambar Zinare a gasar kwallon kwandon da ke gudana a wasannin motsa jikin na Olympics da suka gabata da suka hada wadda China ta karbi bakunci a Beijin a 2008, ta birnin London a 2012, sai kuma ta birnin Rio a 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.