Isa ga babban shafi
Wasanni

Zan ci gaba da buga kwallo har sai na kasa gudu - Ronaldo

Dan wasan gaba na kungiyar Manchester United, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa ba zai yi ritaya daga buga kwallon kafa ba har sai ya ji ba ya iya gudu, sarrafa tamaula wajen yanka da kuma kai wa ragar abokan hamayya hari.

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo Paul ELLIS AFP
Talla

Kaftin din na Portugal ya bayyana haka ne gabanin karawar da kungiyar sa ta United za ta yi da Liverpool a ranar Lahadi.

Yanzu haka dai Ronaldo ke rike da kambin zama dan wasan da ya fi kowa zira kwallaye a matakin kasa da kasa da adadin kwallayen 115 da ya ci wa kasar sa ta Portugal.

A matakin kungiya kuwa, yanzu haka ya ci wa Manchester United kwallaye 6 a kakar wasa ta bana, bayan sake kulla yarjejeniya da ita da yayi daga Juventus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.