Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya fashe da kuka bayan rasa damar zuwa Qatar

Tauraron dan kwallon Manchester United Cristiano Ronaldo ya fashe da kuka yayin da Serbia ta lallasa Portugal da ci 2-1 a gidansu inda ta samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a badi.

Dan wasan gaba na tawagar Portugal Cristiano Ronaldo, yayin wasan da Sebia da hanasu samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya 2022 a Qatar, a wasan da aka tashi 2-1 ranar 14/11/21.
Dan wasan gaba na tawagar Portugal Cristiano Ronaldo, yayin wasan da Sebia da hanasu samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya 2022 a Qatar, a wasan da aka tashi 2-1 ranar 14/11/21. PATRICIA DE MELO MOREIRA AFP
Talla

Portugal ta shiga fafatawar ta jiya da bukatar maki daya kacal don samun tikitin shiga gasar cin kofin duniyar, amma koma ta gaza kai bantenta har akayi nasara a kanta.

Mintuna biyu da soma wasa Renato Sanches ya ci wa Pourtugal kwallon daya tilo da ta zura, Sai dai Serbia ta ki bada gari inda tsohon dan wasan Southampton Dusan Tadic ya rama kwallon kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Ana daf da Karkare wasa Mitrovic, wanda a bara ya barar da bugun fanareti mai muhimmacin yayin da Serbia ta sha kashi a hannun Scotland a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai na Euro 2020, ya yi nasarar zura kwallo da ta baiwa kasarsa damar samun tikitin zuwa Qatar a badi.

Ronaldo ya fashe da kuka

Daga nan ne kyamarori suka koma kan Ronaldo, wanda ke wurga hannayensa cikin bacin rai yana zubda hawaye.

kasashen da suka fice 

A yanzu Portugal ta bi sahun kasashe irinsu Sweden, Wales, Switzerland da Italiya, Finland ko Ukraine, Scotland, Turkiyya, Norway da Netherlands, sai kuma Rasha, Poland ko Ingila, da Arewacin Macedonia da Romania da suka rasa damar shiga gasar na neman cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.