Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta baiwa tsohon kocin Real Madrid jagorancin tawagar Super Eagles

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta nada Jose Peseiro dan kasar Portugal a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafar kasar ta Super Eagles.

Sabon mai horas da tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles Jose Peseiro.
Sabon mai horas da tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles Jose Peseiro. Nelson ALMEIDA AFP
Talla

A ranar Laraba ne dai, hukumar ta NFF ta tabbatar da sabon nadin bayan taron zartaswar da ta gudanar.

Sai dai, a cewar hukumar kwallon Najeriyar, Kocin Rikon Kwarya Augustine Eguavoen ne zai jagoranci ‘yan wasan kassar na Super Eagles zuwa gasar cin kofin kasashen Afirka ta AFCON da za a fara a Kamaru, yayin da shi kuma sabon kocin tawagar na dindindin Mista Peseiro zai yi musu rakiya ne kawai, domin sa ido kan yadda lamurra za su gudana.

Da zarar kuma an kamala gasar ta AFCON zai fara aiki gadan gadan a matsayin babban kocin ‘yan wasan Najeriya.

Jose Peseiro.
Jose Peseiro. © Reuters

Daga cikin fitattun ayyukan sabon kocin Najeriyar akwai zamansa mataimakin mai horas da kungiyar Real Madrid da ke gasar La Liga a shekarar 2003, inda yayi aiki tare da Carlos Queiroz, a karkashinsu ne kuma Madrid din ta lashe gasar La Liga, to amma daga bisani kungiyar ta sallame su, bayan gaza lashe kofin La Ligar a kakar wasa ta 2004 lokacub da Valencia ta yi nasarar lashe kofin.

Baya ga rike mukamin mataimakin Real Madrid, Peseiro ya hora da kungiyoyi da dama a kasashen Girka da Romania da Masar, da kuma tawagar kwallon kaafar kasar Saudiya, kafin daga bisani ya koma Portugal inda ya horas kungiyar FC Porto a shekarar 2016.

Aiki na karshe da Jose Peseiro yayi shin a na horas da tawagar kwallon kasar Venezuela inda ya ajiye aiki a watan Agustan shekarar 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.