Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Sierra Leone ta hana Algeria sakat a wasansu da aka tashi babu kwallo

Algeria mai rike da kambun gasar cin kofin Afrika ta tashi wasa babu kwallo ko guda a karawarta da Sierra Leone yau talata karkashin rukuninsu na E da ya kunshi kasashen Ivory Coast da Equatorial Guinea.

An tashi wasa babu kwallo tsakanin Algeria da Sierra Leone.
An tashi wasa babu kwallo tsakanin Algeria da Sierra Leone. CHARLY TRIBALLEAU AFP
Talla

A zagayen farko na karawar Leone Stars ta fi nuna bajinta kuma ta samu damarmaki musamman ta hannun dan wassanta Alhaji Kamara wanda ya kai kwararan farmaki har sau 2.

Sai dai a zagaye na biyu Algeria ke da wasa a hannu amma kuma mai tsaron ragar Leon Stars Mohamed Nbalie Kamara ya hana Yacine Brahimi da Riyad Mahrez damar zura kwallo bayan doke kwallaye da dama.

Tsohon dan wasan Ingila Steven Caulker da ya sauya kasa zuwa Sierra Leone ya nuna bajinta a karawar ta yau wajen bayar da tsaro kasancewarsa mai tsaron baya ta yadda ya hana ‘yan wasan gaba na Algeria sakat.

Wannan dai ne karon farko da Sierra Leone ke sanya kafa a gasar tun shekarar 1996.

An dai bayyana mai tsaron raga na Sierra Leone Mohamed Nbalie Kamara a matsayin gwarzon wasan saboda rawar da ya taka wajen hana kasarsa shan kaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.