Isa ga babban shafi

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo ta 700 a matakin kungiya

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin cin kwallo ta 700 a tsawon shekaru kusan 20 da ya shafe yana taka leda a kungiyoyin kwallon kafar da ya haskawa a nahiyar Turai.

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. Action Images via Reuters - CARL RECINE
Talla

Yayin karawar da suka yi ranar Lahadi a gasar Firimiya, Manchester United ta doke Everton da kwallaye 2-1.

Everton ce dai ta fara jefa kwallo a ragar United ta hannun dan wasanta Alex Iwobi na tawagar Super Eagles ta Najeriya, amma daga bisani Antony da Cristiano Ronaldo suka ci kwallaye biyu.

Kwallon ta biyu da Ronaldo ya saka ce ta bashi damar kafa tarihin cin kwallaye 700 jimilla a matakin kungiyoyi, yayin da abokin hamayyarsa Messi ke da 691.

Ronaldo dai ya buga wasa a kungiyoyi hudu da suka hada da Sporting Lisbon da Manchester United wadda ya sake komawa gare ta, sai kuma Real Madrid da Juventus.

Dan wasan ya ci kwallaye 5 a wasanni 31 da ya buga wa Sporting Lisbon, a Real Madrid kuwa kwallaye 450 ya ci a wasanni 438, sai kuma kwallaye 101 a wasanni 134 da ya buga wa Juventus.

A zangon farko da ya bugawa Manchester United, kwallaye 118 Ronaldo ya ci a wasanni 298, yayin da kuma tun bayan sake komawa kungiyar da yayi a farkon kakar wasan da ta gabata, dan wasan ya ci kwallaye 26 a wasanni 48.

A fagen wasanni na kasa da kasa, Ronaldo ya kafa tarihin zura kwallaye 117 daga cikin wasanni 191 da ya buga wa kasarsa Portugal tun a shekarar 2003.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.