Isa ga babban shafi

Kocin Ghana ya zargi Alkalin wasa da fifita Ronaldo a wasansu da Portugal

Mai horar da tawagar kwallon kafar Ghana a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar, Otto Addo ya cacaki alkalin wasansu na jiya dan kasar Amurka game da yadda ya bayar da fenariti ga Cristiano Ronaldo wanda ya bashi damar zura kwallon da ya kafa tarihi da ita, bugun fenaritin da kocin ya bayyana a matsayin kyauta ta musamman daga alkalin ga dan wasan.

Cristiano Ronaldo bayan zura kwallon da ta bashi damar kafa tarihi a gasar cin kofin Duniya.
Cristiano Ronaldo bayan zura kwallon da ta bashi damar kafa tarihi a gasar cin kofin Duniya. © AFP - ODD ANDERSEN
Talla

Kwallon ta Ronaldo da ya ci a bugun na fenariti ta biwa dan wasan na Portugal damar sake kafa tarihin da ya mayar da shi dan wasa na farko da ya ci kwallo a gasar kofin duniya biyar.

Portugal dai ta yi nasara a wasan na jiya kan Ghana da kwallaye 3 da 2, lamarin da ya mayar da ita jagora a rukuninta na H da maki 3.

Wani abin fargaba shi ne, wannan suka da Addo ya yi wa alkalin wasa Ba’amurke, Ismail Elfath ya fito fili sosai, kuma hakan na iya jefa shi cikin matsala da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

Addo ya ce dan wasan bayansa, Mohammed Salisu bai yi wa Ronaldo komai ba, kana ya yi korafin cewa alkalin wasan bai yi amfani da na’uran VAR mai taimakawa alkalin wasa ba.

Kocin mai shekaru 47, wanda wannan ne karon farko da ya ke jagorantar kasar a gasar kofin duniya, ya ce ya so ya gana da alkalin wasan don ya mai tambaya a kan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.