Isa ga babban shafi

Qatar 2022: Ramos ya ci kwallo uku yayin da Portugal tayi waje da Switzerland

Goncalo Ramos ya ba da hujjar maye gurbin Cristiano Ronaldo ta hanyar zura kwallo uku rigis a raga, yayin da Portugal ta lallasa Switzerland da ci 6-1 a ranar Talata.

Goncalo Ramos
Goncalo Ramos REUTERS - CARL RECINE
Talla

Ramos mai shekaru 21, wanda ya fara wasa maimakon Ronaldo, ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya zura kwallaye uku a gasar cin kofin duniya zuwa zagayen dab da na kusa da na karshe, tun bayan Pele a shekarar 1958.

Pepe, Raphael Guerreiro da Rafael Leao suma sun zira kwallaye a ragar Switzerland, inda a yanzu wasanta nag aba Portugal zata fafata ne da Morocco.

Ronaldo, mai shekaru 37, wanda a yanzu baya tare da wata kungiya, tun bayan ya bar Manchester United, ya neman sake kafa wani sabon tarihi a gasar.

Dan wasan daya tilo da ya zura kwallo a gasar cin kofin duniya sau biyar, kocin kasarsa Fernando Santos ya ajiye Ronaldo a benci, bayan ya mayar da martani a fusace sakamakon sauya shi a wasan rukuni na karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.