Isa ga babban shafi

Kasashe 30 sun kalubalanci makomar 'yan Rasha da Belarus a gasar Olympics

Gwamnatocin kasashe sama da 30 sun nemi kwamitin shirya wasannin motsa jiki na Olympics na duniya IOC, da yayi bayani akan yadda ‘yan wasan Rasha da Belarus za su iya shiga gasar a matsayin ‘yan wasa da ba sa wakiltar wata kasa yayin wasannin Olympics din da za a yi a birnin Paris cikin shekarar 2024.

Hedikwatar kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC, da birnin Lausanne a kasar Switzerland.
Hedikwatar kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC, da birnin Lausanne a kasar Switzerland. © REUTERS/Denis Balibouse/Files
Talla

Cikin wata wasika ta hadin gwiwa, kasashen 30 cikinsu har da Faransa, Amurka, Birtaniya da kuma Canada sun nuna damuwa ganin yadda ‘yan wasan na Rasha ke da alaka da sojojin kasarsu da suka mamaye makwafciyarsu Ukraine.

Rasha da kawarta Belarus, wadda ta ba da damar amfani da yankinta a matsayin wurin kaddamar da yaki kan Ukraine a watan Fabrairun da ya gabata, sun fuskanci takunkumin haramta wa ‘yan wasansu na motsa jiki shiga wasannin Olympics.

A baya bayan nan ne kuma kwamitin shirya wasannin na Olympics ya sanar da cewa yana kan nazarin hanyar bai wa ’yan wasan Rasha da Belarus damar shiga gasar da za ta gudana a Paris, amma a karkashin tutar ‘yan ba ruwanmu, matakin da ya fusata Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.