Macron ya kaddamar da kidayar kwanakin gasar Olympics ta Paris 2024
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kaddamar da kidayar kwanakin fara gudanar babbar gasar Olympic ta Paris 2024 a daidai lokacin da hukumomin kasar ke rige-rigen inganta fasalin hanyoyin sufuri na birnin Paris.
Wallafawa ranar:
Mahukuntan Paris na Faransa na son gudanar da gagarumin bikin da ba a taba ganin irinsa ba na bude babbar gasar ta Olympic, yayin da shugaba Macron ya karbi bakwanci masu shirya gasar da ‘yan kasuwa a fadarsa ta Elysee domin tattaunawa game da shirye-shiryen gudanar da ita.
Shugaba Macron ya kuma yi wa daruruwan ma’aikatan gwamnati masu ruwa da tsaki jawabi a shalkwatan jami’an ‘yan sandan Paris da ke kusa da gabar kogin Seine duk dai karkashin shirye-shiryen karbar bakwancin gasar ta Olympic.
Shugaba Macron ya kuma yi tsokaci kan aikin tsaftace kogin Seine wanda ya gurbace soasai a daidai lokacin da ya rage kwanaki 500 a fara gasar ta Olympic.
Mutanen birnin Paris sun jima suna fatan a gyara wannan kogin ta yadda za a ci gaba da yin iyo a cikinsa, inda har a 1988, tsohon shuganban Faransa Jacques Chirac ya yi alkawrin gyara kogin cikin shekaru uku, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.
Sai dai a yanzu, ana ganin babu makawa cewa, za a gyaran kogin na Seine saboda Faransa na son a gudanar da wasu wasanni na iyo a kogin a yayin gasar ta Paris 2024 kuma tuni aka ware euro biliyan 1 da miliyan 400 saboda tsaftace kogin kadai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu