Isa ga babban shafi

Thomas Tuchel ya zama sabon kocin Bayern Munich

Bayern Munich ta kori kocinta Julian Nagelsmann, bayan kasa da shekaru biyu yana jagorantar kungiyar, inda ta maye gurbin sa da  Thomas Tuchel wanda zai ga ragamarta daga nan zuwa 2025.

Thomas Tuchel, tsohon Chelsea da PSG.
Thomas Tuchel, tsohon Chelsea da PSG. © AFP - PAUL ELLIS
Talla

Tsohon kocin dan asalin kasar Jamus, ya samu nasarar lashe gasar  Bundesliga ga kungiyar, inda yanzu haka Munich ta kasance ta biyu a saman teburi, wato maki daya tsakanin ta da Borussia Dortmund, wadda ke mataki na daya.

Bayern Munich dai ta doke Paris St-Germain a gasar cin kofin nahiyar zakarun Turai, wanda hakan ya bata damar tsallaka wa zagayen dab da na karshe, inda yanzu haka za ta fafata da Manchester City a gasar.

A watan Satumba ne, kungiyar Chelsea da ke buga Premier Ingila ta sallami Tuchel.

Yanzu haka dai, Tuchel ya maye gurbin Nagelsmann wanda ya karbi ragamar kungiyar a watan Yulin 2021, kuma kwantaragin sa zai kare ne a ranar 30 ga watan Yunin 2025.

Bayern Munich ta ce, sabon kocin zai fara jan ragamar kungiyar ne a ranar Litinin.

Haka zalika Munich, ta kuma tabbatar da cewa, masu taimaka wa kocin, Dino Toppmoller, Benjamin Gluck da kuma Xaver Zembrod sun bar kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.