Isa ga babban shafi

Falasdinawa za su koma buga wasannin kwallon kafa a Algeria

Algeria ta amince ta rika karbar bakuncin dukkanin wasannin da tawagar kwallon kafar yankin Falasdinawa za ta rika bugawa.

'Yan wasan kwallon kafa na yankin Falasdinawa.
'Yan wasan kwallon kafa na yankin Falasdinawa. © AP
Talla

Hukumar kwallon kafar yankin Falasdinu, wadda filin wasanta ke Yammacin Kogin Jordan ce ta nemi taimako daga kasashe domin karbar bakuncin wasannin da tawagarta za ta rika bugawa saboda kazancewar da rikici ke yi tsakanin Hamas da Isra’ila.

Daga ranar 16 ga watan Nuwamba, tawagar kwallon yankin Falasdinawan za ta fara buga wasannin neman tikitin halartar gasar cin kofin duniya ta 2026, inda za ta kara da Lebanon.

A ranar 21 ga Nuwamban kuma Falasdinawan za su karbi bakuncin tawagar kwallon takwarorinsu na Australia, wasan da za a fafata a Algeria.

A halin yanzu Algerian da yankin na Falasdinu na dakon amincewar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA kan shirin nasu.

A makon da ya gabata yankin Falasdinu ya janye daga  wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Merdeka da ake buga wa a Malaysia don sada zumunci tsakanin kasashe ko yankuna kimanin 3 ko sama da haka, sakamakon tsanantar hare-haren ramuwar da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan Zirin Gaza, bayan farmakin da Hamas ta kai mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.