Isa ga babban shafi

Foden da Bellingham na rige-rigen samun rigar Ingila lamba 10

Dai dai lokacin da Manchester City da Real Madrid ke shirin haduwa yau a zagaye na 2 na wasan gab da na kusa da karshe na gasar cin kofin zakarun Turai, hankali ya karkata don ganin wadda za ta fitar da wata, bayan da kungiyoyin biyu suka yi canjaras da kwallo 3 da 3 a haduwarsu ta farko.

Jude Bellingham da Phil Foden na shirin nuna bajinta don karawa kansu kima a tawagar kasa.
Jude Bellingham da Phil Foden na shirin nuna bajinta don karawa kansu kima a tawagar kasa. REUTERS - Juan Medina
Talla

Wani batu mai jan hankali shi ne yadda haduwar ta yau a bangare guda za ta kasance gwaji tsakanin zaratan ‘yan wasan Ingila 2 wato Phil Foden na City da Jude Bellingham na Madrid lura da yadda ‘yan wasan biyu yanzu haka kowannensu ke harin riga mai lamba 10 a tawagar kasa.

Phil Foden zai yi amfani da damar wasan na yau don nuna bajintarsa kan Bellingham.
Phil Foden zai yi amfani da damar wasan na yau don nuna bajintarsa kan Bellingham. POOL/AFP

‘Yan wasan biyu kowannensu na nuna bajinta a kungiyarsa inda Foden ya zama mafi zarra a wannan kaka tsakanin ‘yan wasan City bayan da ya ke ci gaba da cirewa kungiyar kitse a wuta, a bangare guda bajintar Bellingham ta ja hankalin daukacin Turai bayan da ya fara kafa mabanbantan tarihi tun bayan isarshi Real Madrid.

Dukkanin ‘yan wasan dai na matsayin kwarin gwiwar Ingila a wasannin da ke tunkarota na gasar cin kofin Euro wato euro 2024, sai dai abin tambayar shi ne wa zai sanyawa tawagar ta Gareth Southgate riga mai lamba 10?

Ko a haduwar bangarorin cikin makon jiya, Foden ya zura kwallo tare da lashe kyautar dan wasa mafi hazaka a karawar, a bangare guda Bellingham ke ci gaba da kasancewa a sahun ‘yan gaba-gaba na ‘yan wasan da Real Madrid ke amfani da su a kusan kowacce kara.

Bayan haskawa a wasannin lig daban daban da kuma na gasar ta zakarun Turai da ya kai ga zura kwallaye 24 tare da taimakawa a zura wasu 16 cikin wannan kaka, Bellingham zai kuma kasance cikin tawagar da yanzu haka ta isa Manchester don taka leda a Etihad anjima a kadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.