Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

UEFA za ta saurari karar Ibrahimovic game da haramta mai buga wasa

Hukumar dake shirya gasar Zakarun nahiyar Turai ta UEFA, ta ce za ta saurari daukaka karar da dan wasan Paris Saint Germain, Zlatan Ibrahimovic ya shigar, dake neman ta duba hukuncin haramta mai buga wasanni biyu da aka yi, bayan an nuna mai katin kora a wasan da suka buga da Valencia a ran 16 ga watan Febrairu.

Talla

Club din ta PSG ta nemi da a takaita haramta buga wasanni biyu zuwa wasa daya ga dan wasan, domin hakan zai bashi damar buga wasan da PSG za ta yi da Barcelona a zagayen quarter finals na Champions League a ran 2 ga watan Aprilu.

Dan shekaru 31, Ibrahimovic sau goma sha biyu ya taba samun jan kati a rayuwarsa ta kwallo, sai dai bai taba samu ba a matakin bugawa kasarsa ta Sweden wasa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.