Isa ga babban shafi
Syria

Mutane 6,000 suka mutu cikin watan Maris a rikicin Syria

Masu sa ido a rikicin Syria sun ce sama da mutane 6,000 suka mutu a watan Maris wanda shi ne wata mafi muni tun fara kaddamar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Bashar al Assad.

Wasu da suka rasa rayukansu ta sanadiyar rikicin Syria
Wasu da suka rasa rayukansu ta sanadiyar rikicin Syria REUTERS/Zain Karam
Talla

Hukumar da ke sa ido a rikicikin na Syria ta ce yawancin wadanda suka mutu sun hada da mata 291 da yara kanana 298, da ‘Yan tawaye 1,486 sai kuma dakarun gwamnati 1,464.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 7,000 ne aka kashe a Syria tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar al Assad a watan Maris
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.