Bankunan Switzerland sun amince su fitar da bayanan masu ajiya
Bankunan a kasar Switzerland, sun amince su bayyana sunayen masu ajiyan kudade tare da su, bayan matsin lamba da suka samu daga wasu kashen duniya. Hukumar hadin gwiwar bunkasa tattalin arziki ta duniya ce, ta tilastawa bankunan kasar na Switzerland, da su fitar da bayanai domin a gano wadanda ke gujewa biyan haraji.
Wallafawa ranar:
Tuni dai hakan ya jawo cecekuce a kasar a yayin da wasu masana tattalin arziki suka nuna cewa dole ne bankunan su amince da hakan, wasu na ganin hakan bai dace ba, domin ya sabawa dokar sirrin dake tsakanin mai ajiya da bankinsa.
Ajiya a bankunan kasar ta Switzerland daga wasu kasashen duniya ba sabon abu bane, musamman ga manyan ma’aikatan gwamnatoci daban daban ke zuwa ajiyan kudade.
A ‘yan kwanakin nan an sallami tsohon Ministan kasafin kudin Faransa, Jerome Cahuzac bayan an same shi da laifin ajiya wasu kudade a wani bankin kasar ta Swtizrland a boye.
Kasashen Amurka da Faransa da Birtaniya na daga cikin kasashen duniyan da suka bukaci bankunan na Switzerland da su fitar da bayanan masu ajiya a bankunan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu