Isa ga babban shafi
Switzerland

Za a tursasa bankunan Switzerland su ba da bayanan ma’aikatansu

Akwai yiwuwar za a tursasa bankunan Switzerland dake zaune a kasar Amurka, su bayyana sunan ma’aikatansu a wata yarjejeniya Amurkan ta yi da bankunan wanda ke kokarin kawo karshen badakalar kaucewa biyan kudin haraji da kasar ke fama da shi.

Daya daga cikin bankunan kasar Switzerland
Daya daga cikin bankunan kasar Switzerland www.google.fr
Talla

Wata jarida da ake kira Tages Anzeiger ta bayyana hakan inda ta ruwaito cewa za a bukaci bankunan a Amurka su bayar da bayanansu ga hukumomin kasar.

Ta kuma ruwaito cewa bankunan za su biya diyya ga wasu ma’aikatansu domin bayar da bayanan nasu da bankunan su ka yi.

Fadar Washington ta jima ta na zargin bankunan kasar na Switzerland wajen hada kai da masu kaucewa biyan kudaden haraji a kasar ta Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.