Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Binciken badakala dangane da covid 19 a Faransa

Babban mai gabatar da kara a Faransa yace ya kaddamar da bincike domin gano irin rawar da gwamnati ta taka wajen tinkarar annobar coronavirus wadda ta kashe mutane kusan 30,000 a kasar don gano ko jami’an gwamnati sun yi sakacin da za’a tuhume su da laifin salwantar da rayuka.

Asibitin  Saint-Antoine a birnin Paris na kasar Faransa
Asibitin Saint-Antoine a birnin Paris na kasar Faransa Selbymay/Wikimedia/CC BY-SA 3.0
Talla

Alkali mai shigar da kara a Paris Remy Heitz a ranar litinin ya sanar da kaddamar da bincike don gano gaskiyar tuhume-tuhume dangane da badakala da ake sa ran ta wakana a lokaci bulluwar Covid-19 a Faransa.

Karraraki da dama ne aka shigar da su a ofishin alkali a birnin Paris, koken da ya shafi musaman lokacin da aka takaita zirga-zirgar jama’a, kaddamar da wannan bincike daga ofishin mai shigar da kara zai taimaka don gano irin tsuwa-tsuwa da suka gudana a wancan lokaci.

Kotu ta bayyana cewa wannan bincike ba zai shafi Shugaban kasar ba, bale gwamnatin shugaba Emmanuel Macron wacce ke fuskantar karraraki kusan 80.

Hukumar dake yaki da miyagun dabi’u da suka shafi muhali da kuma lafiyar jama’a ce za ta dukkufa don duba irin koma baya da aka samu tun bayan bulluwar cutar musaman a duniyar ma’aikata, banda haka za ta duba irin hanyoyin da aka bi wajen rabon kelayen rufe kare kai daga kamuwa da cutar.

Indan har ta tabbata cewa an tafka ba dai dai ba,hakan ba zai sa kotu daukar mataki saman wani ba,sai dai hakan zai taimaka don gano irin banar da aka tafka a lokacin, indan ta kama a kawo gyara, nauyi yah au kan hukumomin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.