Dakarun Afghanistan sun kashe daya daga cikin shugabannin Al Qaeda
Dakarun Afghanistan sun sanar da kashe daya daga cikin manyan shugabannin kungiyar Al Qaeda da Amurka ke nema ruwa a jallo, Abu Muhsin al-Masari, yayin da gwamnatin kasar ke zargin kungiyar Taliban cewar har yanzu tana alaka da kungiyoyin ‘Yan ta’adda.
Wallafawa ranar:
Hukumar leken asirin kasar ta bayyana al-Masari wanda dan kasar Masar ne a matsayin shugaba na biyu a Yankin India dake jagorancin kungiyar, kuma an hallaka shi ne a Yankin Ghazni.
Ministan cikin gida Masoud Andarabi yace kashe al-Masari ya dada fito da dangantaka tsakanin Taliban da Al Qaeda dake yakar gwamnatin Afghanistan.
Baiwa mayakan Al Qaeda wurin zama shine dalilin da ya sa Amurka ta kaddamar da hare hare da mamaye kasar Afghanistan bayan harin da aka kai mata na 11 ga watan Satumabr shekarar 2011.
Yanzu haka Amurkar da kungiyar Taliban sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya wanda zai sa dakarun Amurka da NATO su fice daga cikin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu