Isa ga babban shafi
Hungary

‘Yan sanda na arangama da Bakin haure a Hungary

Rikici ya barke tsakanin ‘Yan Sanda kasar hungary da Bakin haure da ke zanga-zangar hana su shiga Iyarkar kasar daga Serbia, inda rahotanni ke cewa bakin haure na amfani da manya duwatsu wajen jifan Jami’an tsaron da ke kokarin tarwatsu da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi.

Arangama tsakanin Bakin haure da 'yan sanda a kan Iyakar Hungary
Arangama tsakanin Bakin haure da 'yan sanda a kan Iyakar Hungary Reuters/路透社
Talla

A cewar ‘Yan sanda Hungary Bakin haure sun Fusata ne bayan hanasu kutsa kai cikin Hungary, saboda yawan su, lamarin da ya sa suke amfani da duwatsu, sanduna da kwalabe wajen jefe jami’an tsaro da ke datse su shiga kasar.

Rigimar da ke zuwa bayan ‘Yan sanda kasar sun ce za su hukunta bakin haure 316 da suka lalata shingen wayar da aka kafa a kan iyakar kasar da Serbia, Wakilin Kamfanin dilanci labaran Faransa ya rawaito cewa sama da bakin haure 300 ne suka shiga zanga-zangar.

Yayyin da kanana yaran ke kuka sakamakon hayaki mai sa hawaye da ake jefa musu, wanda ke da illa ga lafiya.

Bakin haure dai a yanzu na neman sabbin hanya kutsawa yammacin turai bayan Hungary ta hana su shiga kasar ta.

Tuni shima dai Firaministan Slovakia Roberto Fico ya bayyana furgaban kan halin da Turai ke neman fadawa sakamakon wannan al’amari musaman fanin tsaro da kuma tattalin arziki.

Rahotanni kasashen turai na cewa mafi yawa daga cikin Bakin haure da ke kwarara nahiyarsu na dauke da matsalar kwakwalwa sakamakon kunci da damuwa da suke ciki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.